Wednesday, 8 August 2018

Musha Dariya: Direban Legas Daban Ya Ke A Cikin Sauran Direbobi

Wani direba ne a Legas, ’yan sanda suka tsare shi suka ce ya yi laifi, don haka sai ya ba su Naira dubu hamsin ko su kai shi Alausa.

Ya hada su da Allah su kyale shi suka ce: “Ai mu ba aikin Allah muke yi ba.” Nan da nan sai ya kama dariya, ya dauko wayarsa ya fara magana, yana cewa: “Ranka ya dade, saura minti 30 su fashe, amma bama-bamai 20 ne kawai na dauko, sun ce za su kai motar Alausa, ina nan dawowa da rai yanzu.”


Kafin ka ce kwabo, ’yan sandan nan duk sun tsere. Direba ya gama wayarsa ta karya ya wuce da motarsa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: