Mutane da dama a shafukan yanar gizo sun gasgata ingancin wannan mai wajen kara tsaho da laushin gashi. Haka zalika za a iya shafa shi a jiki da daddare idan za a kwanta, wanda a nan ma yana taimakawa fata wajen kara laushi da rage alamun tsufa.
Ga abubuwan da ake bukata
- Karas
- Man zaitun ko man kwakwa
- Fiya (Avocado)
Yadda ake hadawa
- Da farko za a goga karas din da dan dama sannan a bare fiya guda daya a cire kwallon ciki.
- A dora kasko a wuta, amma ba mai zafi ba sosai.
- A zuba man kwakwa ko man zaitun din a cikin kwaskon, shima da dam dama
- Sai a zuba karas da fiyan a cikin man a barshi ya soyu a cikin man
- Ana yi ana juyawa a hankali
- Ya kan dauki lokaci saboda wutar ba mai zafi ake bukata ba.
- Idan ya soyu, sai a tace shi a bari ya huce.
- A juye shi a cikin kwalba mai murfi.
Hanyoyin amfani da shi
- Za a iya shafa shi kwana daya kafin ranar da za a wanke gashi. Idan aka shafa sai a rufe da leda a kwana da shi. Washegari sai a wanke gashin.
- Za a iya amfani da shi a matsayin man kitso
- Za a iya shafa shi a jiki da daddare a kwana da shi, da safe a wanke.
0 comments: