Kungiyar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta yi kira ga mutane da su rage yawan cin gishiri domin guje wa kamuwa da cututtukan dake kama zuciya.
Kungiyar ta bayyana haka a shafinta na tiwita inda ta ce yawan cin gishiri a abinci na kawo wa zuciyar mutum matsala da idan ba a kula ba yakan yi ajalin mutum.
Domin guje wa irin haka, kamata ya yi mutane musamman matasa su ci akalla cikin karamin chokali daya a rana idan ya kama, hakan zai taimaka wurin kare zuciyar mutum sannan da kare mutum daga kamuwa da cututtuka kamar su hawan jini, shanyewar sashen jiki da sauran su.
WHO ta kuma bayyana cewa mutane za su iya inganta kiwon lafiyar su ta hanyar cin ganyayyakin da kuma kayan lambu.
Sannan idan har ta kama a ci gishirin kamata ya yi a ci wanda ke dauke da sinadarin ‘Iodine’ domin shi wannan sinadarin na taimaka wa wurin kar kaifin kwakwalwar yara kanana da jaririn dake cikin iyayen su mata.

0 comments: