- Barawon ya rasa ransa ta dalilin hakan
- Lamarin ya faru ne a jihar Filato
Wasu dakarun sojin Najeriya dake a wata runduna ta musamman dake aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato sun kashe wani matashi mai shekaru 18 a duniya da gwale-gwale sakamakon zargin sa da akayi da satar wayar Salula.
Lamarin dai kamar yadda muka samu ya faru ne a karamar hukumar Bokkos ta jihar kuma matashin da ya rasa ransa sunan sa Amadu Atajan wanda bai dade da kammala karatun sa na makarantar gaba da Sakandire ba.
Al'ummar gari dai da ma kungiyoyi da dama sun nuna takaicin su game da lamarin sannan kuma suka bukaci gwamnati da ta gaggauta yin bincike da zummar hukunta duk masu hannu a ciki.
A wani labarin kuma, Dakarun sojin Najeriya dake fafutukar ganin sun kakkabe dukkan barbashin 'yan ta'addan Boko Haram sun sanar da samun nasarar kashe manyan kwamandojin 'yan ta'addan uku yayin wani artabu da sukayi da su a garin Bama.
Babban daraktan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar, Texas Chukwu shine ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a ranar Juma'ar da ta gabata.
0 comments: