Mambobi 5000 na jam'iyyar PDP sun sauye sheƙa zuwa APC a jihar Legas
Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, akwai kimanin mambobi 5000 na jam'iyyar adawa ta PDP da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC cikin jihar Legas a ranar Juma'ar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, shugaban jam'iyyar reshen jihar, Alhaji Tunde Balogun, shine ya yi lale maraba da masu sauyin sheƙar a shelkwatar jam'iyyar dake jihar ta Legas.
a ranar 3 ga watan Yulin da ta gabata wasu mambobi 500 na jam'iyyar PDP suka sauya sheka daga jam'iyyar ta PDP zuwa APC a jihar Legas.
Shugaban kungiyar United Niger Delta Forum, Mista Gabriel Ese, shine ya jagorancin mambobin kungiyar sa zuwa jam'iyyar ta APC inda Mista Balogun da wasu jiga-jigan jam'iyyar suka karbe su hannu biyu-biyu.
Cikin jawaban sa yayin karbar masu sauyin sheƙar, Mista Balogun ya bayyana cewa, yana matukar farin cikin dangane da wannan shawara da suka yanke tare da yaba ma su kan amincewar su da jam'iyyar ta APC.
ficewar bazata ta tsohon gwamnan jihar Delta, Emmanuel Uduaghan, daga jam'iyyar PDP ta zamto abin ban mamaki gami da girgiza ga mambobinta tare da fargaba mamayar da jam'iyyar APC za ta yi a jihar.
0 comments: