Sunday, 16 September 2018

Abubuwa 7 Ababen Lura A Lokacin Da Ka Samu Kanka Cikin Damuwa

A duk lokacin da ka samu kanka cikin kunci, tsanani, wahalar rayuwa ko damuwa, kar ka manta da wadannan nan abubuwa guda 7 da zan bayyana. Ko shakka babu za su kai ka ga samun waraka da yardar Allah.

Yi nazarinsu a tsanake:

*1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.*

*2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.*

*3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.*

*4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.*

*5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.*

*6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (ga lada, ga kuma yayewar tsananin).*

*7. Ka tuna cewar Allah shi ne ARHAMANUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.*

_Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don hasken Alqur’aninka, don Rahamar nan taka wacce ta yalwace dukkan halittunka amin_
Barkammu da war haka

Yusuf Sani

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: