Sunday, 16 September 2018

Masana Sun Gano Maganin Da Ke Kawar Da Yiwuwar Kamuwa Da Cututtukan Zuciya

Wasu masana kimiyyar lafiya sun gano hadin magunguna na musamman da ke kawar da yiwuwar kamuwa da cututtukan zuciya.
Masanan na jami’ar ‘Queen Mary’ da ke birnin London a kasar Birtaniya sun ce wannan magani na samuwa ne ta hanyar hada magungunan rage cututtukan da ke kama zuciya da wadanda ke hana kitse taruwa a zuciya.

Daya daga cikin masanan mai suna Ajay Gupta shi ya bayyana haka a wani taron masana kimiyya da aka yi a garin Munich da ke kasar Jamus.


Gupta ya ce sun gwada wannan magani akan tsoffi masu shekaru 60 kuma an samu nasara.

Ya ce sakamakon da suka samu a gwajin ya nuna cewa har wadannan mutane suka kai shekaru 75 zuwa 80 ba su kamu da wata cuta da ke kama zuciya ba ko me sanya shanyewar bangaren jiki.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: