Ali Nuhu Jarumin Kannywood zai samu kyautar karammawa ta musaman daga BON
Bana bikin zai samu jagoranci daga fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau tare da jarumin Nollywood Gbenro Ajibade.
Fittacen jarumi kuma babban gwanin masana'antar kannywood Ali Nuhu » yana daya daga cikin fitattun jarumai Nijeriya da zasu amshi kyautar karammawa a bikin baiwa fitattun jarumai na kasa kyauta watau BON Awards.
Bikin baiwa fitattun jarumai kyauta ta BON, biki ne wanda ake shiryawa domin fitar da gwanaye cikin yan fim na kasar baki daya bisa ga rawar da suka taka a shirye-shirye daban daban cikin shekara daya. Bikin wanda aka fara cikin shekara 2009 yana gudana a ko wace shekara.
Ma'aikacin wanda ke shirya bikin Seun Oloketuyi yace za'a baiwa Ali Nuhu tare da fitacciyar jaruma
Omotola Jalade ekehind e tare da babban direkta
Lancelot Imaseun kyauta ta musamman domin karrama su bisa ga rawan da suke takawa a fanin nishadantarwa.
"Ali Nuhu ya karfafa gwiwan yan arewa da dama wajen samun aiki a Nollywood. Don haka shi tauraro ne kuma jarumi mai kaurin suna ga yan arewa." Oloketuyi yace.
Rahama Sadau zata jagoranci bikin bana
Bana bikin zai samu jagoranci daga fitacciyar jarumar Kannywood Rahama Sadau tare da jarumin Nollywood Gbenro Ajibade.
Ita ma Rahama tana cikin yan takarar amsar kyauta a bikin a bangare mata kan shirin "TATU" wanda ta nuna kwarewarta a harkar fim tare da basirar da Allah ya bata.
Za'a gabatar da bikin ranar 16 ga watan disamba a Abeokuta babban birnin jihar Ogun .
0 comments: