Friday, 21 September 2018

Adam A.Zango "Bana siyasa don kudi kuma babu wanda ya biyani kudi na yi wa Buhari waka"



Mawakin ya bayyana hakan ne bayan fitar sabbin wakoki da yayi ma shugaba Buhari da Mallam Nasir El-ruafai gabanin zaben 2019.

Gabanin fitowar sabbin wakokin shi mawaki yace a ringa kiran shi 'Ranka shi dade'  (Instagram/adam_a_zango)
Mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Adam Abdullahi Zango wanda aka fi sani da A.Zango ya karyata zarge-zarge da ake masa na karban kudi domin yin wakar siyasa.
Zargin ya biyo bayan wani bidiyo da ya wallafa a shafin sa inda yake bin sabon wakar da yayi ma shugaba Buhari.

A wani sako da ya kara wallafa a shafin sa, Zango yace yana goyon bayan zarcewar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai domin sune zabin sa kuma zai cigaba da goyon bayan anniyar su gabanin zaben 2019.

Yana mai cewa "Bana siyasa don kudi.... Kuma babu wanda ya biyani nayiwa BABA buhari da mallam nasiru el'rufai waka!!.They are my choice & I will give them my support!!".

Ya kara da cewa kowa na da ra'ayin bin duk wanda yake so.

Mawakin ya fitar da wasu sabbin wakoki da ya rera na neman zarcewar shugaba Buhari.

Ga taken Wakokin kamar haka; 'Likitan Gyaran Nigeria' da 'Mu zabi Baba' da 'Tsintsiyace Alheri' sai kuma 'Kaduna sai mallam'.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: