Thursday, 20 September 2018

Aisha Muhammed Maganar cewa ana lalata da mata a masana'antar kannywood karya ne


Jaruman tace wasu yan bata gari ke yada jita-jita domin su lika ma masana’antar sharri bisa ga barnar da suke
Jaruma Aisha Muhammed ta bayyana cewa jita-jitan dake yaduwa na cewa sai anyi lalata da mata ake basu damar fitowa a shirin fim na masana’antar shirya fina-finai na kannywood karya ne kuma babu kamshin haka a masana’antar.

Ta fadi haka ne yayin wani hira ta musamman da tayi da Daily nigeria, Tana cewa;

“Tunda na shiga kannywood har na samu damar damawa da gummain masana’antar ban taba gani ko inji inda aka yi lalata da wani domin samun damar fitowa a wani shiri, maganar banza ce”.

Ni dai ban taba ganin inda haka ya faru tsakanin jaruman masana’antar. Kowa yana aiki shi yadda ya kamata kuma ma’aikatan suna bada nasu taimakon kamar yadda ya kamata. Babu wanda ya nemi ni da haka kuma ban taba gani da ido na cewa ana ma wata haka.”

“Wasu yan hana ruwa gudu masu aikata ire-iren haka ke neman gurbatar da wannan masana’antar”.

Aisha wadda ta shiga masana’antar kannywood cikin 2016 ta fara fitowa cikin fina-finai da dama ciki har ma da wadda ta shirya da kanta.

Masu sharhi suna ganin cewa nan gaba Aisha zata yi kakara cikin masana’antar da ire-iren su Nafeesa Abdullahi, Rahama Sadau, Halima Atete da dai sauran su.

Jaruma mai neman ficewa haifaffen yar garin Jos dake jihar Filato ce amma tayi karatun firamari da sekandere a garin Tafa dake jihar Kaduna . Tana aji 5 a sekandere iyayen ta suka yi mata aure.

Bayan fitowar ta daga gidan miji kasancewa auren bai tafi yadda ya kamata shine ta nema yadda zata fara harkar fim don tun tana yar karama take da burin yin fim.

Ta cinma burin ta yayin da Usman Mu’azu na kamfanin express media arts ya gabatar da ita cikin masana’antar kuma shirin da ta fara fitowa a cikin shine “safara” tare da fitaccen jarumi Adam A.Zango.

“Abun ya bani mamaki sosai da aka bani damar fitowa tare da Zango, ban taba tunanin haka. Kawai a waje na dauke shi cewa kaddara ce daga Allah” inji Aisha.
Bayan ta nuna ma masu shirya fina-finai cewa hakika tana iya damawa cikin masana’antar wannan sabon jaruma ta samu dama na fitowa a cikin wasu shirin fim daban-daban.

Cikin fina-finai da Aisha zata fito akwai Safara, Meera, Madadi, Tsohon Najadu, Kare Jin da Garba Gurmi .

Aisha tayi kira ga sauran yan wasa na masana’antar kannywood da su tallafa wajen kare mutuncin yan masana’antar

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: