Bakar uwa: Wata mata ta sayar da yaronta akan N350,000 don ta yi shagalin kirsimeti da kudi
Wata mata, Oluchi Mba ta sayar da yaronta mai shekaru 7 da hauhuwa akan kudi N350,000.
- Rundunar yan sanda ta ce wadanda ake zargin an cafke su, tare da cewar an kwato yaron daga hannun su.
- Rundunar ta ce za a gurfanar da masu laifin gaban kotu da zaran an kammala bincike
mata mai shekaru 28 da ke da zama a Ogidi, karamar hukumar Idemili ta Arewa, jihar Anambra, Oluchi Mba ta sayar da yaronta mai shekaru 7 da hauhuwa akan kudi N350,000.
Naij.com ta tattara rahoton cewa, Mba ta yanke wannan hukunci ne a kokarin da ta ke yi na tara kudin da zata yi shagalin bikin kirismeti na wannan shekarar, wanda ya sa ta sayar da yaron nata mai shekaru 7 da hauhuwa akan N350,000.
Wata majiya ta labarta yadda matar ta ke ta dokin zata yi shagalin kirismetin na wannan shekarar a watanni uku masu zuwa cikin wadatar kudi, kafin daga bisani yan sanda su cafke ta.
0 comments: