Saturday, 22 September 2018

An Yankewa Wani Dan Kasuwa Hukuncin Daurin Shekaru 140 A Gidan Yari

Mai shari’a Mohammed Idris na babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a jahar Lagos, ya yankewa wani dan kasuwa hukuncin daurin shekaru 140 a gidan yari.
An kama dan kasuwan ne da laifuka 13 da suka jibanci coge da damfara.

Hukumar yaki da cin anci ta EFCC ita ta guranar da mutumin mai sune Jones Biyere a gaban kuliya tun a shekarar 2013.


Hukuncin ya kunshi na shekaru 10 akan kowanni laifi daga na 1 zuwa 11. Sai kuma shekaru 15 akan laifi na 12 da 1 kowannensu, wanda gaba daya idan aka hada ya kai shekaru 140 a gidan yari.

Biyere zai yi zaman kurkukun a jere.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: