Saturday, 15 September 2018

Illar Auren Dole Ga Maza

Idan masu karatun wannan shafin ba su manta ba, a kwanakin baya na yi wani rubutu a game da illar yin auren dole ga mata, inda na tabo illolin da hakan ke haifarwa sannan na yi alkawarin zan tabo bangaren yadda ake yi wa maza auren dole. Lalle iyaye su rika yin taka-tsan-tsan a game da yadda suke aurar da ’ya’yansu maza da mata don a samu zamantakewar aure mai dorewa ba kamar yadda ake yawan samun saki a tsakanin ma’aurata a wannan zamani ba musamman ma a bangaren Hausawa ko a Arewacin kasar nan.

Bincike ya nuna auren dole na daga cikin abin dake haifar da yawan saki a al’ummar Hausawa da kuma yankin Arewacin kasar nan. Don haka a yau sharhi na zai karkata ne kacokal a game da yadda ake yi wa wasu maza auren dole da kuma bala’in da hakan ke haifarwa kamar haka:

Saki: Kamar yadda na ambata a farkon bayani na, daya daga cikin kalubalen da al’ummarmu ta Hausawa ke fuskanta ita ce ta yadda wasu iyaye kan dage lallai sai dansu ya auri wata mace da watakila ba shi da ra’ayinta ko kadan. Akan samu wadansu ’ya’yan saboda biyayyar da suke yi ga iyayen nasu, sukan hakura da irin matan da iyayensu kan aura musu, amma mafi yawa daga ciki ba kasafai suke bin umarnin iyayen nasu ba. Wadanda ma suka hakuran, to ba a son ransu suke zaune da matan ba.

Hakan ce ke janyo ake yawan samun saki da bayan an yi auren. Da ma tun farko an yi auren ne ba bisa soyayya da kaunar juna ba. Za ta iya kasancewa ita macen tana son mijin, amma shi ba ya kaunarta a cikin zuciyarsa ko kadan. Ka ga a nan dole ne a samu matsala. Idan ana so a samu ingantaccen aure dole ne a samu amincewa a tsakanin ma’auratan biyu. A yi shi cikin soyayya da kwanciyar hankali da kuma amincewar juna. Don haka a takaice dai za a iya cewa auren dole na daga cikin abin da ke kawo saki a tsakanin ma’aurata a kasar Hausa.


Cutarwa: daya daga cikin illolin da auren dole kan janyo a cikin al’umma shi ne cutarwa da wasu mazan kan yi wa matan. Cutarwa ta kunshi rashin ciyarwa ko tufatarwa ko bayar da cikakkiyar kulawa da sauransu. Mazan da ake musu auren dole a mafi yawan lokuta ba kasafai suke damuwa da halin da matan nasu ke shiga ba.

Hasalima wasu sukan shafe lokaci mai tsawo ba tare da sun waiwayi gida ba. Sukan ce idan sun koma gida maimakon su kasance cikin farin ciki, to suna kasancewa ne cikin bakin ciki a koda yaushe, saboda kiyayyar da suke wa matan. Idan kuwa haka ne, to mene ne amfanin irin wannan auren? Hausawa kan ce da muguwar rawa gwamma kin tashi. Akwai wadanda kan shafe fiye da shekara daya ba tare da sun koma gida ba, saboda an yi musu auren dole. Lallai cutarwa ta shigo a wannan fage.

Rashin Burgewa: Wani al’amari game da yi wa maza auren dole shi ne rashin burgewar da matan ke yi musu. Duk iya kwalliyar mace ko iya girki ko iya magana ko iya kwanciya ga wasu mata, muddin an yi auren ne ba bisa yarda da soyayya a tsakaninsu ba, to za ka tarar matar ba kasafai take burge mijin ba, don shi a ganinsa tamkar yana hada ido da wata kasurgumar macijiya ce. Duk abin da matar ta yi masa don ta burge shi, shi a wajen irin wannan miji, ba za ta taba burge shi ba.

Don haka ya kamata iyaye su rika neman amincewar ’ya’yansu a duk lokacin da za su hada su aure don kada daga baya a koma ana yin da-na-sani. Akwai wani labari makamancin wannan da wani ya taba ba ni inda ya ce abin ya faru da gaske.

Wani abokinsa ne aka yi wa auren dole, amma saboda biyayya irin ta iyaye sai ya amince aka yi auren, amma daga baya ya koma yana cutar da matar a asirce. Ya nuna yadda ya kan kwashe wata da watanni ba tare da ya kusanci matar don yin ibadar aure ba. Ya kan kwashe watanni ba tare da ya ci abincin da ta girka masa ba, kai hasalima ya ce duk abin da ta yi masa ba ta taba burge shi ba, da ya ga dai abin ya ki ci ya ki cinyewa sai ya sallame ta, ta hanyar sakinta ba tare da iyayensa sun sani ba. Daga baya ne iyayen suka samu labarin abin da ya faru kuma suka nuna fushinsu a kan matakin da ya dauka ba tare da ya sanar da su ba. Sun yi kokarin sasanta mijin da matar don ta koma gidan mijin amma ita matar da kanta ta sanar da iyayenta gaskiyar lamari, kuma ta nuna atabau ba za ta koma gidansa ba, don ta yi nadamar auren da aka hada ta da shi.

Iyayen yarinyar da na mijin suka zauna suka fahimci juna daga karshe dai tilas aka hakura da wannan aure. Ba a dade ba Allah ya fito mata da miji shi kuma ya auri wata matar da yake so daban. Daga karshe dai dukkansu sun samu kwanciyar hankali da farin ciki a sabon auren da kowannensu ya yi. A nan ne iyayen suka gane kuskurensu kuma suka yi alkawarin hakan ba za ta sake faruwa ba.

Yawaitar Zaurawa: Daga cikin abin dake sanyawa ake yawan samun mace-macen aure kuma ake samun zaurawa masu yawa a cikin al’umma, akwai yi wa maza auren dole. Igiyar aure dai a hannun miji take, don haka wasu mazan da sun ji duku-duku sukan dauki matakin saki ne ba tare da la’akari da me hakan zai janyo a cikin al’umma ba. Batun yawan zaurawa a kasar Hausa dai ya zama ruwan dare, don da wuya mutum ya leka wani lungu ko sako bai tarar da mata zaurawa da suka taba yin aure aka sako su ba. To in kuwa haka ne, me kake ganin zai faru a al’ummar da ’yan mata suka yi yawa ba mijin aure sannan ga zaurawa su ma sun karu bayan an sako su daga gidajen aure? Fasadi da alfasha ne za su wanzu a tsakanin al’umma. Wannan kuma babbar illa ce a cikin al’umma. Don haka ba a ce iyaye kada su shiga gaba wajen aurar da ’ya’yansu maza da mata ga wadanda suke ganin sun fi cancanta ba, amma a rika yin taka-tsan-tsan wajen tursasawa ’ya’yan game da auren dole. Iyaye su sani lokaci ya canza, a da akwai tarbiyya da bin umarnin iyaye da ’ya’ya kan yi, amma a wannan zamani karancin tarbiyya ta janyo ’ya’ya kadan ne ke jin maganar iyayensu ballantana har su amince da bukatar iyayen nasu game da yi musu auren dole.

Iyaye su sani mene ne amfani badi ba rai ?
Ka aurar da ’yarka ba a dade ba kuma an sako maka ita har ma tare da ciki ko kuma ma da ’ya’ya ?

Ya dace mu yi karatun ta-natsu don mu samu al’umma tagari da za mu rika alfahari da ita. Allah ya sa kowa ya auri wanda yake so shima kuma ta ke son shi, amin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: