Yan fashi sun afka gidan shahararren maibada umarni na Kannywood -Yakubu M. Kumo
Barayin sun far ma gidan sa ne a daren ranar talata 11 ga watan Satumba inda suka yi awon gaba da abubuwa da zasu iya daukawa.
Wasu yan fashi da makami sun kai hari gidan shahararren marubucin hausa na masana'antar Kannywood wato Yakubu M Kumo.
Barayin sun far ma gidan sa ne a daren ranar talata 11 ga watan Satumba inda suka yi awon gaba da abubuwa da zasu iya daukawa.
Kamar yadda abokin sana'ar shi Ibrahim Birniwa ya bayyana a shafin sa na Instagram Kumo ya dan samu rauni wajen gwagwarmaya da yayi dasu wajen tokare kofar falonsa don hana su shiga.
Abun godiya game da fashin shine ganin cewa barayin basu ji masa mummunar rauni wanda har sai an kwantar dashi a asibiti.
0 comments: