Monday, 3 September 2018

Jerin shugabannin kasashe 9 da suka kawowa Buhari ziyara cikin watanni biyu kacal

Yayinda zaben 2019 ke gabatowa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da hadimansa na yada nasarori da ya samu a shekaru uku zuwa yanzu da dau ragamar mulki a shekarar 2015.

Daga cikin abubuwan da ake ganin nasara ne shine karin farin jini da Najeriya ta samu daga shugabannin kasashe daban-daban a fadin duniya. Hakan ya sa shugabannin na zuwa Najeriya don hada zumunci da Buhari da kuma ganewa idanuwansu irin hadaka da alfanun da za'a samu.

A watanni biyu kasacl da suka gabata, akalla shugabannin kasashen Afrika da Turai tara sun kawowa Buhari ziyara Najeriya.

Karanta jerin shugabannin:
1. Shugaban kasar Togo, Faure Ganssingbe: A ranan 29 ga watan Yuni, shugaban kasar Togo ya kawo ziyarar ban girma ga shugaba Buhari a jihar Katsina.

2. Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron: A ranan 3 ga watan Yuli, shugaban kasar Faransa. ya kawo ziyarar ban girma da yarejejeniya kan bunkasa kasuwanci da hannun jari tsakanin Najeriya da Faransa

3. Shugaban kasan Namibia, Hage Gottfried Geingos: A ranan 4 ga watan Yuli, shugaban kasar Namibia ya kawo nasa ziyarar.
4. Shugaban kasar Arika a kudu, Cyril Ramaphosa: A ranar 11 ga watan Yuli, shugaban kasar Afrika ta ya yi zuwarsa Najeriya ta farko bayan zama shugaban kasa.

5. Shugaban kasar Niger, Mahamaou Issoufu: Kasancewa makwabcin Najeriya, shugaban kasar Nijar ya kawo nasa ziyarar da ya saba.
6. Shugaban kasar Benin, Patrice Talon: A ranan 23 ga watan Yuli, shugaban kasar Benin da ke makwabtaka da Najeriya ya kawo nasa ziyarar.
7. Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow: Ranan 1 ga watan Agusta, shugaban kasar Gambia, ya yi zuwarsa Najeriya na farko tun bayan kwace mulki daga hannun tsohon shugaba Yahya Jammeh.
Jerin shugabannin kasashe 9 da suka kawowa Buhari ziyara cikin watanni biyu kacal

8. Firam Ministan Birtaniya, Theresa May: A ranan 29 ga watan Agusta, firam ministan Birtaniya, Theresa May, ta kawo ziyarar birnin tarayya Abuja da jihar Legas inda ta gana da yan kasuwa masu hannu da shuni irisu Dangote da sauransu.


9. Shugabar Jamus, Angela Merkel: A ranan 31 ga watan Agusta, shugabar Jamus ta kawo ziyararta Najeriya domin bunkasa zumunci kasuwanci da tattalin arziki.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: