Sunday, 2 September 2018

Kabilar Igbo zata zabi Buhari a 2019 don kaucewa kuskurenta na 2015


- Kungiyar G-23 ta ce kabilar Igbo ba zata sake tafka babban kuskuren da ta yi a zaben 2015 ba, in da ta zabi siyasar kabilanci akan cancanta

- Shugaban kungiyar na shiyyar Kudu maso Gabas, Onunkwo, ya bayyana hakan ga manema labarai a jihar Ribers

- Kungiyar ta kuma yi alkawarin yin aiki kafada da kafada da shugaban kasa Muhammadu Buhari a sake zabensa 2019 a Kudu maso Gabashin kasar

Kungiyar dake kare muradun shugaban kasa Muhammadu Buhari, G-23, ta ce kabilar Igbo ba zata sake yin dambarwar da tayi a zaben 2015 ba, inda ta zabi yin siyasar kabilanci mai maikon zaben cancanta, kamar dai yadda ta zabi tsohon shugaban kasa Jonathan kawai saboda bangarancin shiyya.

Kungiyar ta nuna nadamar abubuwan da suka faru a wancan lokacin, da suka shafi gurguncewar siyasar Kudu maso Gabashin kasar, inda ta ce kabilar Igbo zasu fito kwansu da kwarkwatarsu don marawa Buhari baya, na yin tazarce a zaben 2019.

Shugaban kungiyar G-23 a Kudu maso Gabas, Johnbosco Onunkwo, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fatakwal, jihar Rivers, a ranar asabar, ya ce gwamnatin shugaban kasa Buhari ta bunkasa yankin Kudu maso Gabas dama kasar baki daya, wanda ala tilas ne a sake bata wata damar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: