Saturday, 1 September 2018

Wata Sabuwa: Yawan Bani-Bani Yasa Na Yiwa Mata Ta Karyar Na Mutu

Rahoto daga Premium Times ta bayyana cewa wani dan kasar Honduras mazaunin kasar Amurka mai suna Danny Gonzalez ya karyata mutuwarsa domin guje wa yawan bani-bani daga wurin matar sa.


Gonzalez na daya daga cikin ‘yan kasar Honduras da iyalen su ke dogaro da su sanadiyyar zaman da suke yi a can kasar Amurka.

Gonzalez ya ce tun da ya koma zama a kasar Amurka matar sa ta zama aljihu da kulum sai dai a zuba masa kudi.

Ya ce “Duk ranar Asabar matata kan kira ni a waya sannan duk kiran da za ta yi mun na tambayar kudi ne daga nan kuma babu abin da zai sake hada ni da ita.

“Ganin yawan bani-bani din da matata ke yi ya ishe ni sai na dauki wannan mataki na in karyata mutuwa ta.

Ai ko bayan ya aika mata da hotunan sa kwance kamar gawa, sai ko ‘yan uwansa suka rude, suka fara neman yadda za suyi su tabbatar da haka. Jaridu suma basu bar maganar ta wuce haka kawai ba.

Daga baya sai aka gano cewa ashe bai mutu ba yana nan da ran sa lafiya sumul. Matar sa ce kawai ya nemi ya tada wa hankali ko ya huta da tambaya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: