Rundunar yansandan jihar Ogun ta cafke wani Malamin Chochi dan shekara 42 mai suna Olusola Akindele tare da wani da suka aikata laifin tare Ayodele Bamiduro dan shekara 42 bayan Olusola ya kashe wata mata mai suna Iya Aanu yar shekara 40, ya sare kanta daga bisani ya bizine gawarta a wani kangon gida a bayan gidansa.
Olusola dai daya daga cikin Malaman Chochin Lion of Judah Church of Christ ne wanda ke lamba 13, Robiyan Avenue, Robiyan, kusa da Ijoko a jihar Ogun.
Bayanai sun ce mariganyar masoyiyar Olusola ce, kuma sun shafe shekara biyu suna soyayya. Ranar 30 ga watan Juli, Iya Aanu ta kai ma saurayinta Olusola ziyara a gidansa da ke Mosefajo, kamar yadda aka saba, bayan sun gama saduwa, sai Iya Aanu ta zauna a gefen gado tsirara domin ta dan huta.
Daga nan ne Olusola ya zagaya ya zaro wata guntuwar tabarya ya kwantara mata a kai iya karfinsa, sakamakon haka Iya Aanu ta sheka lahira.Daga bisaani Olusola ya ja gawarta ya kaita cikin dakin wanka, ya sare kanta da hannaye, bayan haka kuma ya je ya bizine gawarta a wani kangon gida da ke bayan gidanshi.
Karanta wannan: Shugabanin APC Uku Sun Mutu A Wani Mumunan Hatsari Daga Madina Zuwa Makka
Asiri ya tonu ne bayan wani shugaban alumma a yankin ya kai kara wajen yansanda cewa an gano gawar wata mace da ta fara rubewa a unguwar, kuma gawar bata da kai domin an gundule. Sakamakon haka ne yansanda suka shiga bincike da ya kai su ga kama Olusola.
Kwamishinan yansanda na jihar Ogun CP Iiyasu, ya shawarci jama’a su dinga shaida wa akalla mutun daya wajenda zasu je ko wajen waye zasu je domin kauce wa bata gari.
MALAMIN CHOCHI YA Malamin chochi ya kashe masoyiyarsa ya gundule kai ya bizineta a bayan gidansa.
Ga hotunan a kasa;

0 comments: