Sunday, 16 September 2018

Musha Dariya: Bakatsine Tare Da Budurwarsa... Ana Wata Ga Wata

Wani Bakatsine ya je hira wajen budurwarsa, bayan sun gama zai tafi sai ya sa hannu a aljihu ya dauko kudi ya ba ta. Sai budurwar ta ce ba za ta karba ba. Shi kuma ya ce:“To tun da ba ki so, ni ma ba na so.”


Sai ya yi watsi da kudin a nan, kowa ya kama gabansa. To ashe ita wannan budurwa ba tafiya ta yi ba, ta dan labe ne a wani waje a gidan, da niyyar idan saurayin ya tafi ta zo ta kwashe kudin.


Haka shi ma Bakatsine bai tafi ba, ya dan labe a kofar gidan da niyyar idan yarinyar ta shiga gidan ya zo ya kwashe kudinsa.

To dama a cikin soro suke zancen kuma an dauke wuta, can sai saurayin da budurwar suka dawo cikin soron, suka fara laluben kudin ba tare da kowannensu ya ga dan uwansa ba.

Can sai aka kawo wuta, nan take sai Bakatsine ya wayance ya ce wa budurwar: “Don Allah ba ki ga wayata ba?” Ita ma budurwar ta ce masa: “Ni ma don Allah ba ka ga sarkata ba?

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: