Monday, 17 September 2018

Subahanallah! An kama dan majalisa tsirara yana wanka a kasuwa cikin tsakar dare



Dan majalisar mai suna Timothy Owoeye shine shugaban jam'iyar mafi rinjaye a majalisar dokokin jihar Osun.
Dubun wani dan majalisar jihar ta cika yayin da yaci karo da fusatattun matasa a daidai inda yake wanka a kasuwa tsakar dare.

A labarin da Laila News ta fitar dan majalisar mai suna Timothy Owoeye shine shugaban jam'iyar mafi rinjaye a majalisar dokokin jihar Osun.

Jami'an tsaro na kasuwar Osunjela dake garin
Oshogbo suka kama dan majalisar yayin da suke sintiri .

Dan majalisar yana wakiltar yankin Ilesa ta gabas a majalisar dokokin jiha karkashin jam'iya mai mulki ta APC.

Yayin da harkar siyasa ya kara kamari bisa ga matsowar zaben 2019, wasu daga cikin abubuwa da wannan lokacin ke haifarwa shine labarin tsubbu da asiri.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: