Sunday, 16 September 2018

Yadda Zaku yi Maganin Amosanin ka

Amosani ciwo ne da ke sanya fatar kai bushewa tare da kaikayi. Har yanzu masu binciken kimiyya da likitoci basu gano takamamen abinda ke janyo amosani ba amma akwai wasu abubuwa da ke sanya amosanin ya karu idan ba'a kiyaye ba.

Abubuwan da ke kara yaduwarsa sun hada da

1) Rashin tsafta (2)Garkuwar jiki mara karfi (3) Damuwa mai tsanani (4) Yanayin garin (tsananin zafi ko sanyi) (5) Maikon fata (6) Yin amfani da abubuwan wanke kai da bai karbi jikin mutum ba

Alamun da mutum zai gane yana da amosani shine zai rika yawan ganin fatar kansa bushewa tana sauka masa a kafada kuma kansa zai rika masa kaikayi. Wasu lokutan amosanin yakan kai ga zuwa gira da kunuwa.

Yadda ake magance Amosani

Amosani abu ne mai wuyan magani farat daya amma ana iya daukan matakai da na samun saukinsa sosai.

1) Wanke kai da Shampoo: Yin amfani da Shampoo yakan rage dati da maiko da ke daskarewa a kan mutum hakan kuma sai sanya fatar kan mutum da kasance cikin lafiya. Da ya ke akwai Shampoo din daban-daban sai mutum ya karanta ka'idar yadda ake amfani da irin wanda ya siya.

2) Rage damuwa: Yawan damuwa yana haifar da cututuka da yawa, duk da cewa damuwa kanta bata janyo amosanin, takan gurgunta garkuwar jikin mutum kuma hakan zai rage wa jikin dan adam karfin yaki da cutar.

3) Amfani da man kwakwa: Man kwakwa na daya daga cikin ababen da ake amfani dashi wajen maganin amosanin kai saboda yana dauke da sinadaren da ke hana fatar kai bushewa karara

4) Kauracewa tsananin zafi ko sanyi: Jikin mutum musaman fatarsa tana son zama cikin yanayi na tsaki-tsaki ne, saboda haka zai mutum ya yi kokarin kiyayewa.

5) A tafi wajen Likita: Idan mutum ya kiyaye dukkan ababen da muka ambata kuma amosanin nasa baiyi sauki ba sai ya garzaya asibiti wajen likita domin a duba shi a bashi magunguna.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: