SIRRIN RIKE MIJI: MATAKAN MALLAKAR MIJI Daya bayan daya
SHEIKH JA'AFAR MAHMOUD ADAM
(Fitowa na (001)
Ku sani cewa ita rayuwa ta auratayya,
rayuwa ce wadda take ibada, wani fanni
ne mai zaman kansa wanda ake bukatar
ma'aurata su kasance sun kware a cikinsa,
domin su gudanar da shi bisa ga tsari.
Mu sani rayuwa ta auratayya babban
abin da ta ke ginuwa akan sa ita ce
"SOYAYYA". Da dai shari'a ba ta yadda ayi
aure ba bisa ga tilas, a shari'a ba tilasta wa
namiji ko mace don su auri juna, sai dai aja
hankalinta ko hankalinsa har ya yarda ko ta
yarda don ta aure shi ko ya aure ta.
Shi ya sa lokacin Annabi (S A W) da aka
daura auren wata budurwa sai taje wajen
Manzon Allah (S A W) cewa: gashi fa
iyayenta sun yi mata auren tilas, sai Annabi
(S A W) ya ce, mata kina da za6i, ko ki aure
shi, ko kuma kice ba ki yarda ba, dole a
sake ki".
Sai wannan yarinya ta ce: "Wallahi zan iya
hakuri zama da shi, amma abin da yasa
nayi wannan kara sai don iyaye su ji daga
bakinka cewa: basu da damar tilasta wa
"ya ta auri wanda ba ta so".
Wannan hadisi yana tabbata ce daga
bakin Manzon Allah ( S A W).
Kuma ku sani ita "Kauna" (Soyayya)
sakamakonta ne duniya ta ke zama lafiya.
Duk lokacin da aka nemi "Kauna" ko (Soyayya) aka rasa, to sai a dinga samun
yawan fadace fadace da kuma yawan
tashin hankali.
Good post, arewarmu.
ReplyDeleteKaranta: Sirrikan Mallakar Miji a musulince na har abada.