SURA DA SIFFOFIN UWA TA GARI
LALLE
Yar’uwata ki sani lalle kwalliyace
ga duk ya mace kuma mace idan ta
bar hannunta ko kafarta ba lalle to
ba’a iya banbance ta da namiji.
Kuma kowace irin kalan lalle da
mata sukeyi kema kiyi da zaran ya
goge sa ki biyoshi da wani kala
domin cika siffarki ta ya mace.
BANGAREN ADO
Yar uwa ki sani kirkire
kirkiren adon zamani wajibine
akanki a gidan mijinki harma da
irin naki salon adon, kuma duk
wata dressing da mata sukeyi a
duniya dolene ki rinka yiwa mijinki
matukar bai sabawa addinin
musulunci ba, sannan kiyi masa
ado da duk irin kayan da kika
mallaka.
KISISINA DA KARERAYA
Ya yar’uwata mace bata cika
mace ba idan bata iya kisisina irin
ta mata ba, kamar su kareraya,
yanga da rigima. Kuma ki sani irin
wadannan dabi’un su suke
daukaka martabar mace a wurin
mijinta acikin dukkan alamuran su,
Magana ko tafiya ko kallo da
makamantansu.
DAMUWA DA DAMUWARSA
Yar uwa wajibine ki karanci halin
mijinki sosai kisan mijinki acikin
halin farin ciki da kuma bakin ciki
kuma ki lura da yanayin sa a
lokuta kamar haka:
Ø Lokacin fita nema
Ø Lokacin dawowa daga nema
Ø Lokacin gajiya
Ø Lokacin farin ciki
Ø Lokacin bakin ciki
Ø LOKACIN FITA NEMA:
A wannanl okaci yaruwata ki sani dolene
ki tabbata mijinki ya fita daga
gida cikin kwanciyan hankali da
natsuwa. Akwai wani dabi’a da
matan magabata sukeyiwa
mazajensu, su kan shirya bayan
sunyi wanka da kwalliya sannan
sai su raka mazan su har kofar
gida ko kofar daki, sannan suna
tafiya suna taku daddaya da
rangwadi kuma su kan yimusu
addu’a sannan su basu wasiyan
cewa idan Allah yasa ka samu
halal ka kawo mana, idan kuwa
baka samu ba zamuyi hakuri da
azabar yunwa akan azabar
Allah. Bayan ya fita yayi nisa sai
ki kirashi da wani sunan
soyayya mai dadi sai kiyi masa
Kiss da hannunki. Sai kice masa
Allah ya bada sa’a. Allah ya sa
mudace Ameen.
Ø LOKACIN DAWOWA DAGA NEMA:
Kisani yar’uwata miji yana
dawowa gida a halin gajiya
kafin ya dawo kin shirya ma
dawowarsa.
Ø LOKACIN GAJIYA:
A wanna lokaci ki
sani zaki nemi ruwa mai dumi a
lokacin sanyi idan kuma lokacin
zafine, sai kinemo ruwan sanyi
ki kai masa wurin wanka bayan
ya gama wankan ya dawo daki
ki bashi abinci
Ø LOKACIN FARIN CIKI :
Yar’uwata a
wannan lokacine zaki baje kolin
shagwabar ki da rungumarsa
Ø LOKACIN BAKINCIKI :
Yar’uwata a
wannan hali babu wasa babu
tsokana a tsakaninku har sai
kinji mai ya bata masa rai, idan
ya fita bai samo bane sai ki
kwantar masa da hankali, sai ki
nuna masa kullum Allah yana
basa sai kawai don yau baka
samo ba sai muyi hakuri mu
godewa Allah. Idan kuwa wani
ne ya bata masa rai, sai ki bashi
hakuri da kuma kwantar masa
da hankali, sannan idan ya
dawo miki cikin tashin hankali
sai ki warware masa bayan kinji
mai ya faru dashi. Idan ba zaki
iya warware masa ba sai ki
kaishi inda za’a warware masa
damuwarsa.
IYA ABINCHI
Rashida wallahi wannan shine
babban hanyar sace zuciyar miji
idan har kin iya abinci sosai,
wallahi sai dai kiji mijinki yana cin
abinci yana santi yana kuma cewa
amarya Allah ya miki Albarka
harma ya miki kyauta sakamakon
santin cin abincin. Sannan ba zai
taba jin tsoron duk bakon da akayi
ba ta bangaren abinci kam ko da
kinyi masa laifi sai yace ya yafe
saboda santin abincin.
0 comments: