YADDA AKE HADA HUMRA FARA, DA BAKA {culucture} TURAREN WUTA. NA KAYA DA NA TSUGUNO
turaren alajin na ruwa ko na marakana ko na matan arewa
✭ jan ambur
✭ farin ambur
✭ misik
✭ madarar turaren kwamando
✭ madarar turaren suzan
✭ madarar turaren sarkin turare
✭ madarar turaren sandol
✭ madarar turaren ismiyaki
zaki yi ki daka farin ambar dinki wanda ake sayarwa a kasuwa guda uku,
sannan ki daka jan dan kanti guda uku, sai ki zuba a kan ruwan turaren alajin
ko marajana ko matan arewa roba daya, ki sami misik dinki guda hudu ki
zuba a kofin silver ko a tukunyar silver ki dora a kan garwashi zai narke, idan
ya narke sai ki yi sauri ki juye a cikin ruwan turaren da kika zuba garin
abubuwan, sannan ki daka misik din ki sa cokali uku sannan ki zuba madarorin turaranki ko wanne cikin kwalbar fiya-fiya ki jua sosai ki rufe ya tsumu, wannan garin misik dinda ambar din shi zai dinga kara tsuma humra ta
dinga kara kamshi za ki iya rufewa kwana bakwai ko zuwa sati biyu ta tsumu
0 comments: