Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da takardun makarantar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bace bat Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana, inji rahoton The Cables.
Adesina ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka yi dashi da jaridar The Nation, inda yace maganar ta mutu, an wuce wajen, kuma duk masu tayar da maganar marasa aikin yi ne.
Idan za’a tuna shugaba Buhari bai mika takardunsa dake nuna shaidar cewa ya kammala karatun sakandire ba, wanda kuma shine karancin matakin karatun da dokokin Najeriya suka amince dan takara ya taka kafin ya taka takarar shugaban kasa.
Don haka ne wannan lamari ya tayar da kura matukar gaske a dandalin siyasar Najeriya, inda wasu suka tubure lallai sai Buhari ya bayyana takardunsa, amma Adesina ya mayar musu da martani, inda yake cewa:“Maganar takardun karatun Buhari ya wuce,marasa aikin yi ne kawai ke cigaba da ruruta ta, tun kafin zaben shekarar 2015 aka kashe maganar, ina ganin masu tayar da maganar nan sun fahimci zasu sha kayi a zaben 2019 ne, don haka suke neman tudun dafawa
“A lokacin da Buhari da sa’anninsa suka shiga aikin Soja, sai aka amshe musu takardunsu na asali, hatta tsohon shugaban hafsan hafsoshin Sojan Najeriya, Alani Akinrinade ya tabbatar da batun amshe takardun nasu, don haka hukumar Soji ta san inda takardun suke.
“A lokacin da Buhari da sa’anninsa suka shiga aikin Soja, sai aka amshe musu takardunsu na asali, hatta tsohon shugaban hafsan hafsoshin Sojan Najeriya, Alani Akinrinade ya tabbatar da batun amshe takardun nasu, don haka hukumar Soji ta san inda takardun suke.
“Amma hukumar tace ta tabbatar da takardun, don haka, haka baya nufin Buhari bai yi makaranta ba, tun da har ya zana jarabawar kammala sakandari, kuma ya ci, sa’annan ya halarci horo daban daban, hatta kwalejin yaki ta Birtaniya ya je.”Inji shi.
Daga karshe Kaakakin ya ce akwai wadanda suke ganin Buhari bai je makaranta ba, har ma suka garzaya gaban Kotu, kuma kotu ta bayyana cewa basu da gaskiya.
0 comments: