Idan ba a maida albashi N30, 000 ba; za a gani a akwatin zabe Inji NLC
Mun samu labari daga Jaridar Vanguard cewa Kungiyar NLC ta ‘Yan kwadago a Najeriya ta tubure a kan batun karin albashin Ma’aikata inda ta nuna cewa idan fa har ba ayi kari ba, APC za ta rasa kuri’u.
NLC ta taso Buhari a gaba tace idan babu karin albashi babu kuri'a a zabe
Jagororin Kungiyar NLC sun yi zanga-zanga a sassan Kasar nan jiya inda su ka nuna cewa ba za su yi na’am da wata magana ba illa a maida karancin albashin Ma’aikaci ya zama N30, 000 a kasar nan ko kuma Gwamnati ta ji jiki a 2019.
Kungiyar NLC da na TUC da ma UCL sun fito sun yi zanga-zanga a manyen Biranen Najeriya jiya yayin da su ke kara shiryawa yajin aikin da za a iya shiga a makon gobe muddin Gwamnati ba ta kara albashi kamar yadda su ke nema ba.
Ma’aikatan sun shelantawa Gwamnatin Najeriya cewa idan har ba a dabbaka yarjejeniyar da aka yi na kara albashi zuwa N30, 000 a kowane wata ba, to babu shakka ba za su zabi wannan Gwamnati mai-mulki ta zarce a 2019 ba.
‘Yan Kwadagon sun kuma nuna cewa ba za su koma tebur da Gwamnati ba domin kuwa kwamitin da aka nada a baya ta kammala duk wata tattaunawa. Fustattun Ma’aikatan sun zargi Ministan kwadago Chris Ngige da rashin tausayi.
A Ranar Talatan nan ne Gwamnonin Jihohin Najeriya su ka zauna game da lamarin inda su ka cin ma matsaya ta karshe su kace abin da za su iya biya shi ne N25, 000 a maimakon yadda NLC ta ke nema.
0 comments: