Yadda aka gano gawar janar alkali a Jos bayan watanni da bacewar sa
An gano gawar marigayi Janar Idris Alkali a wata rijiya dake kauyen Gwuchet dake karamar hukumar Jos ta kudu nan jihar Filato ranar Laraba 31 ga watan Oktoba.
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar cewa an gano gawar manjo Janar Idris Alkali bayan wata biyu da sanar da bacewar shi.
na gano gawar shi ne a cikin wata rijiya dake kauyen Gwuchet na gundumar Shen dake karamar hukumar Jos ta kudu nan jihar Filato .
Kwamandan runduna ta uku ta dakarun kasar kuma shugaban bincike domin gano gawar marigayin, Birgediya Janar Umar Mohammed ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Laraba 31 ga watan Oktoba.
Janar Mohammed ya ce an samu wannan nasarar ne bisa ga labari da daya daga cikin wadanda suka mika kansu ga yan sanda ya bada.
Janar Mohammed yana mai cewa "Kamar yadda aka sani, mun sanar da bacewar Manjo Janar Idris Alkali ranar 3 ga watan Satumba."
"Saboda haka ne muka bazama nemansa, kuma mun gano motarsa wadda a cikinta muka gano wasu daga cikin kayansa, kuma wannan ne ya bayyana mana cewa wani mummunan abu ya same shi."
"A makon jiya kuma mun gano wani kabarin da aka tone, wanda ya ta tabbatar mana da cewa an kai gawarsa wani wuri bayan an fara binne ta a wurin."
Yace an mika garzaya da gawar sojan asibiti kuma daga nan za'a sanar da jan'izar sa.
Tuni dai rundunar sojoji ta sanar da neman wasu mutum 13 da suke da hujjar cewa da hannunsu wajen bacewar sojan.
Shugaban dakaru masu bincike yace umarni uku aka basu kuma sun cika biyu. Yace sun gano gawar shi da kuma motar shi wadanda sune na daya da na biyu da aka umarce su suyi.
Kamar yadda ya sanar matakin da ya rage shine hukunta duk wadanda ke da hannu a wajen aikata wannan mummunan laifin.
Ya kara da cewa duk wanda aka samu yana da hannu, komai girmansa sai ya fuskanci hukunci.
0 comments: