Saturday, 10 November 2018

Aisha Buhari ta yiwa wasu 'yan fim sha-tara ta arziki a fadar shugaban kasa (Hotuna)

Aisha Buhari ta yiwa wasu 'yan fim sha-tara ta arziki a fadar shugaban kasa (Hotuna)

A'isha Buhari ta sa labule da wasu 'yan fim a fadar shugaban kasa

- Uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari ta yiwa wasu 'yan fim sha-tara ta arziki
Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Aisha Buhari ta karrama wasu 'yan fim din Hausa a masana'antar Kannywood dake da mazauni a Arewacin Najeriya a fadar shugaban kasa, garin Abuja babban birnin tarayya.

Mun samu cewa uwar gidan shugaban kasar ce ta bayyana hakan a wasu hotuna da ta wallafa a shafin ta na dandalin sadarwar zamani ta Facebook inda take mika masu kyaututtuka bayan sun gama wata muhimmiyar tattaunawa.

Legit.ng Hausa dai ta samu cewa a 'yan kwanaki kadan ma da suka gabata 'yan fim din magoya bayan gwamnatin APC sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa inda suka kaddamar da wata wakar da suka yi wa gwamnatin a matsayin gudummuwar su.

Wa'anda uwar gidan shugaban kasar ta karrama dai sun hada da Ali Nuhu, Naziru Ahmad, Ibrahim Maishunku, Bello Muhammad Bello, Falalu Dorayi da dai sauran su.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: