Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun kai hari a garin Maiduguri
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai wani hari kan mazauna bayan filin wasan Polo da ke Jiddari a garin Maiduguri.
Wani jami'in agaji na farar hula (civilian JTF) ya shaidawa kafar watsa labarai ta YERWA EXPRESS ta wayar tarho cewar mayakan sun kai harin ne da yammacin yau, Asabar.
Kazalika, wani mazaunin unguwar mai suna Muhammad Arabi ya tabbatar da batun kai harin.
Wannan ba shine karo na farko da mayakan kungiyar Boko Haram ke yunkurin kai hari garin Maiduguri ba ta hanyar unguwar Jiddari da ke bayan filin sukuwa.
Za mu kawo ma ku karin bayani....
Saturday, 10 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: