Dan fansho 'ya mutu ya dawo'
Wani mutum a Kazakhtan ya koma gida wata biyu bayan an yi jana'izarsa.
Mutumin wanda dan fansho ne ya koma gida ne tun kafin iyalai da 'yan uwansa su gama alhinin rasuwarsa.
"Lokacin da Baba Aigali ya shigo gida ta kofar baya cikin koshin lafiya bayan mun yi wata biyu da binne shi, 'yata mai suna Saule ta kusa mutuwa sakamakon bugun zuciya da ta gan shi," in ji Esengali Supygaliev a hirar da suka yi da jaridar
Azh.kz da ake wallafawa a shafin intanet.
Mutumin mai shekara 63 ya bar gida ne da safiyar wata rana a watan Yuni kuma tun daga wancan lokacin bai koma ba.
"Da ma dai an san Aigali da yawan ficewa daga gida inda yake shafe mako daya ko biyu bai koma ba ", a cewar Esengali, don haka ne iyalinsa suka jira zuwa wata daya kafin su shaida wa 'yan sanda - wadand suka nuna musu wata gawa da ta kone sosai ko za su gane shi.
Zaman makoki
Hukumomi sun ce gwajin kwayoyin halittar da aka yi kan gawar ya nuna "kashi 99.2 cikin 100 cewa ta Aigali Supygaliev ce' don haka ne aka bai wa iyalansa takardar shaidar mutuwa.
A watan Satumba iyalansa suka binne Aigali a makabartar Musulmi da ke garinsu Tomarly, kusa da kogin Caspia na Atyrau.
" Mun yi masa jana'iza sannan aka yi alhini kamar yadda ake yi a al'adance," inda abokansa suka sha shayi don nuna jimamin rashinsa, in ji Esengali.
Don haka ne lokacin da aka ga shigar gida Aigali wata biyu bayan an yi jana'izarsa sai aka soma tambayarsa abin da ya faru.
Ashe wani mutum ne da suka hadu a kasuwa a kauyen da ke makwabtaka da su ya ba shi aiki. Wata hudu da kammala aikin ne sai Aigali ya koma Tomarly.
'Yan sanda da jami'an ma'aikatar shari'a basu ce komai kan batun ba. Amma masaniyar kimiyyar da ta yi gwajin kwayoyin halitta kan gawar da aka binne ta shaida wa Azh.kz cewa tabbas kashi 99.2 na binciken ya nuna gawar ta Aigali ce ko da yake ta kara da cewa "ya kamata a sani cewa akwai kashi 0.8 na rashin tabbas".
Dangin Aigali sun bayyana bacin ransu kan batun ganin cewa tuni sun bayar da kudin kabari kamar yadda ake yi a al'adance a kasar.
Kazalika sun tambayar cewa. "Shin wanne mutum muka binne?
Saturday, 10 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: