Saturday, 10 November 2018

Fada ya kacame: Ba sauran wani mai tunani da ya rage a jam'iyyar PDP - El-rufai



Gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC, Malam Nasir El-rufai yayi wa jam'iyyar PDP kaca-kaca inda ya ce ba sauran mai tunani da ya rage a jam'iyyar yanzu.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake maida martani ga jam'iyyar ta PDP da a farko ta caccake shi biyo bayan kalaman gwamnan inda ya aibata tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi dake zaman mataimaki ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019.
a jiyan kalaman na gwamnan akan Mista Peter Obi da yace shi mai tsananin kabilanci ne, ya jawo cece-kuce da zafafan kalamai daga al'ummar Najeriya din wanda hakan ne ma ya sa jam'iyyar ta PDP ta fitar da sanarwa dauke da martani zuwa ga gwamnan.

A wani abarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Gombe dake a Arewa maso gabashin Najeriya sun samu nasarar cafke wani malamin Islamiyya mai suna Raudatul Qur’an mai shekaru 26 a duniya da laifin yiwa dalibar sa mai shekaru 5 fyade a ofishin sa.

Jami'an 'yan sandan yayin da suke nunawa manema labarai malamin mai suna Bilyaminu Halilu, tare da sauran masu laifin da suka kama sun bayyana cewa sun cafke shi ne a ranar 1 ga watan Oktoban da ya gabata a garin Gona.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: