Friday, 9 November 2018

Da dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a zaben 2019

Da dumin sa: Hukumar INEC ta wallafa sunayen wadanda za suyi takarar Gwamna a zaben 2019

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) ta soma sakin sunayen wadanda za suyi takarar kujerun gwamnoni a jahohin Najeriya ashirin da hudu da za'a gudanar da zabukan shekarar 2019.

Haka zalika mun samu cewa hukumar zaben har ila yau ta soma fitar da sunayen wadanda za suyi takarar kujerun 'yan majalisun jahohin tarayyar Najeriya dukkan su da za'a gudanar da zabukan su a shekarar ta 2019.

kafin hukumar ta wallafa sunayen, ana ta samun rikice-rikice a jahohi da dama musamman game da 'yan takarkarin gwamnoni na jam'iyyar APC mai mulki wanda har ma ake tunanin rikicin ka iya kara rincabewa.

A wani labarin kuma, Ministan yada abarai na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari Alhaji Lai Mohammed a ranar Laraba ya ce rahoton da kwamitin duba zuwa ga yiwuwar karin alabashin ma'aikata da suka mika wa shugaba Buhari na Naira dubu 30, shawara ce kawai ba wani abu ba.

Ministan yace har yanzu shugaban kasar bai yanke hukunci ba game da matsayar sa akan batun har sai ya yi duba na tsanaki ga rahoton tukuna sannan ya fitar da matsayar sa wadda ake sa ran ta zama ta karshe akan batun.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: