Wednesday, 7 November 2018

Wani sabon salo: Majalisar dokokin Kano ba ta da kayan da za ta binciki Ganduje - Sagay



Shugaban kwamitin shugaban kasa akan yaki da rashawa, Farfesa Itse Sagay (SAAN) ya ce majalisar dokokin jihar Kano ba ta da kayan aikin binciken Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ake zargi da karban cin hanci daga dan kwangila.

Wani bidiyo ya yi fice a yanar gizo inda aka nuna Ganduje yana karban daloli daga hannun dan kwangila, lamarin da ya sa majalisar dokokin jihar kafa kwamitin bincike wanda suka gayyaci gwamnan.
Sai dai wata babbar kotun Jihar Kano ta umurci majalisar dokokin jihar da ta dakatar da binciken a ranar Litinin.

Da yake jawabi da manema labarai a ranar Talata, Sagay ya bayyana cewa bincikn irin wannan bidiyo na bukatar bincike cikin nazari wanda yan majalisar gwamnati ba su isa gudanarwa ba.

Da aka tambaye shi ko yan majalisar gwamnati ba za ta iya bincikar gwamna ba, Sagay ya ce aikin majalisar dokki shine ta yi la’akari da tunani amma ba wai bincikar jami’an jiha ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: