Tuesday, 6 November 2018

YADDA ZAKI DAWO DA NI'IMARKI BAYAN KIN HAIHU

YADDA ZAKI DAWO DA NI'IMARKI BAYAN KIN HAIHU

・✿✿ BAYAN SATI BIYU DA HAIHUWARKI

➽ IDAN KIN HAIHU ➽ sai ki Fara shirya jikinki don tarbar maigida , don in dai lafiya kika haihu Daga lokacin Zaki tsinci kanki cikin kuzari .
Duk wanda ya ganki zai ganki tas kamar ba ki haihu ba .
Don haka tunda tafiyar ta samu sai a Fara shirya jiki , Kiyi kokarin a dafa miki kaza irin ta masu jego ki Fara ci , ( Inda babu kada ki matsawa mijinki ) cin kazar yana Kara gyaran kasan mace maigida yaji ta zam- zam kamar bata haihu ba .
❮❯ shan ya' yan itatuwa akai - akai baran ma ( kankana , abarba , gwada , lemon Zaki .
❮❯ ki dinga yin Kunun aya kina sha. In zai samu Kiyi kullum , Amma karki dinga zuba sukari Dan kadan Zaki dinga sawa ko ki sha haka .
❮❯ shan maganin Mata mai kyau ( habbatus- sauda , Zuma , dabino , aya ,madara , nono Amma me kyau .
❮❯ shan Zuma madi , tsimi da saurabsu .
❮❯ Tun Daga ranar da kika haihu har zuwa lokacin da Zaki yi arba' in ki zama cikin tsaftace jiki da gyaran jiki , gyaran jariri , gyaran gida .

❝ KUMA KARKI YI SAKE DA YIN TURAREN WUTA DANA JIKI DA GIDANKI DA JIKINKI❞

don wasu matan idan suka haihu sai kaganta ( ragajab ba tsaftace jiki ) ko ina su a ganin su idan Ana jego ba a gyaran jiki tunda mijinta Baya tare da su a shimfida , kana zuwa kusa dasu sai kaji wari da karni, wanda a musulinci ko yau mace ta haihu jini ya dauke Mata a ranar data haihu, mijinta yana da ikon zuwa ya sadu da ita a Rana .

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: