Friday, 30 November 2018

Bayan Ziyarar Shugaba Buhari, Boko Haram ta sake kai hari sansanin Dakarun Soji a Arewacin Najeriya



mayakan Boko Haram sun sake kai wani mummunan hari kan sansanin dakarun sojin kasa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya inda Mutane 7

suka jikkata yayin da rai guda ya salwanta.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta AFP ta bayyana a yau Juma'a, wannan hari ya auku bayan kwana guda da taron shugabannin kasashe biyar na nahiyyar Afirka inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a kasar Chadi

Ko shakka ba bu ganawar shugabannin kasashen ta gudana domin tattauna batutuwa da tsare-tsare gami da manufofin kawo gami neman goyon bayan kasashen duniya wajen karshen kungiyar ta'adda ta Boko Haram da a halin yanzu tsagerancinta ke ci gaba da habaka

Harin ya auku ne yayin da mayakan suka ribaci manyan makamai na kare dangi wajen zartar da ta'addanci a sansanin dakarun soji da ke kauyen Arege daura da cibiyar sana'ar Su ta garin Baga a gabar tafkin Chadi.

Majiyar rahoton ta AFP ta bayyana cewa, harin na bazata gami da kwanton bauna ya auku da sanyin Asubahi kamar yadda wani jami'in soji da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayanna

Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun sojin cikin tsayuwar daka ta jiran tsammani da ko ta kwana sun samu nasarar mayar da martani tare da dakile wannan hari da a yayin haka rayuwar daya daga cikin su ta salwanta baya ga jikkatar kimanin dakaru bakwai a filin daga.

harin mayakan Boko Haram a ranar 18 ga watan Nuwamba ya yi matukar muni inda rayukan kimanin Dakaru 43 suka salwanta a sansanin su da ke garin Maitile can jihar Borno daura da iyaka ta kasar Nijar.

Dangane da sabanin rahotanni, wasu daga cikin dakarun da kwanan su ke gaba sun bayyana cewa harin ya salwantar da rayukan fiye da dakaru 100 da a jiya hukumar sojin ta tabbatar da adadin rayukan dakaru 23 kacal da suka salwanta.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: