Hon. Kazaure ya bayyana inda ake samun matsala wajen yakin Boko Haram
Mun samu labari cewa fitaccen ‘Dan Majalisar nan na Jam’iyyar APC, Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure ya nemi Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi maza ya tsige manyan Hafsun Sojojin Najeriya.
A wani bidiyo da ya fito kwanan nan daga hannun Jaridar nan ta Premium Times Hausa, Hon. Gudaji Kazaure yayi wani jawabi inda yake nuna takaicin sa game da irin barnar da ‘Yan ta’addan Boko Haram su ke yi a Kasar nan har gobe.
‘Dan Majalisar na Yankunan Jihar Jigawa ya bayyana cewa babu hadin-kai tsakanin Sojojin sama da kuma Sojojin kasan Najeriya. Kazaure yace wannan ya kawo matsala a wajen yakin da ake yi da ‘Yan ta’addan a Arewa maso Gabas,
Sanannen ‘Dan Majalisar yace abin takaici ne a ce ana rasa Sojojin Najeriya a hannun Boko Haram a karkashin Gwamnatin nan ta Shugaban kasa Buhari. Kazaure yace rashin makamai yana cikin abubuwan da ke hana Sojojin aiki,
‘Dan Majalisar na Jam’iyyar APC mai mulki ya kuma soki ‘Yan uwan sa a Majalisar Tarayya da su ka hana Shugaban kasa Buhari cire makudan Dalolin kudi domin sayawa Sojojin Kasar manyan makamai da sauran kayan aiki kwanakin baya,
Hon. Gudaji Kazaure ya kara da cewa makaman Sojojin na Najeriya sun tsufa, inda yace har yanzu Dakarun Najeriya kan yi aiki da motocin yakin da aka saya a lokacin mulkin Shehu Shagari. A dalilin haka ne ya nemi a sake duba lamarin,
Kazaure yayi kira ga Shugaban kasa ya canza manyan Hafsun Sojin kasar a kawo wasu sababbi dabam. Kazaure wanda ya dade yana rokon a ba sa dama ya shiga Dajin Sambisa ya bayyana cewa a zamanin da, ya kan shiga cikin Dajin Sambisa.
Dazu kun ji cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa a karkashin APGA, Janar John Gbor yace idan har Janar din da ke jagorantar Sojojin kasar nan sun gaza kai Najeriya ga nasara, abin da ya dace ayi shi ne Shugaban kasa Buhari ya canza su.
0 comments: