Yadda wani Saurayi yake soyayya da tsofaffin mata masu shekara 70 ko 90
Wani labari mai ban mamaki ya ratsa Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan inda aka ji labarin wata tsohuwa tu-kuf mai shekaru kusan 100 tana soyayya da wani danyen matashi mai shekaru 30 da haihuwa.
A wani shiri na musamman da ake gabatarwa a Kasar Turai mai suna ‘Extreme Love’, mun ji labarin wata tsohuwa ‘Yar shekara 91 mai suna Marjorie McCool da wani Sahibin ta watau Kyle Jones, wanda ta yi akalla jika da shi.
Shekarun Kyle Jones wanda shi ne Saurayin wannan tsohuwa duka-dauka a Duniya 31, amma dai wannan bai hana su cin karen su babu babbaka ba. Wata Jarida a kasar Birtaniya mai suna Mirror ce dai ta kawo wannan rahoto.
Abin da ya ba mutane mamaki dai shi ne yadda wannan Matashi yake bin tsofaffin mata wanda sun haife sa ko sun yi jika da shi. Kafin ya hadu da Mc Cool, Kyle Jones yayi soyayya da tsofaffi masu shekara 70, 80 ko ma 90 a Duniya.
Kyle Jones yace tun yana ‘Dan shekara 12 zuwa 13 da haihuwa ya fara neman tsofaffin mata wanda shekarun su yayi nisa. Jones ya kuma kara da cewa babu irin matan da yake sha’awa a rayuwar sa kamar wadanda su ka tsufa tu-kuf.
Jones ya bada labarin yadda ya hadu da wannan tsohuwa ya kuma bayyana cewa ta ba sa mamaki a lokacin da su ka tara. Yanzu haka Jones yana soyayya da wata Dattijuwa ‘yar shekara 68 mai suna Anna.
Sunday, 2 December 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: