Sunday, 4 November 2018

Dandalin Kannywood: Abinda ya sa mazaje ke shakkar auren 'yan fim - Kyauta Dillaliya



- Jarumar fina-finan Hausa, Fati Nayo ta bayyana cewar mazaje a kasar hausa suna tsoron auren mata da suka waye
- Ta kuma ce irin yanayin da suke fitowa a fim shima yakansa mutane su rika yi musu shedar da ba haka halinsu ya ke ba
- Jarumar ta shawarci mazajen da ke

kaunar su da aure su rika kusantarsu su san halayensu na gaskiya bai wai jita-jita ba
Shaharariyar jarumar wasan kwaikwayo na Dadin Kowa Sabon Salo da ake nunawa a Arewa 24, Fati Nayo wanda akafi sani da Kyauta Dillaliya ta bayyana cewar sheda mara kyau da al'umma ke musu ne dalilin da yasa mafi yawancin su yin aure da wuri.

Kyauta Dillaliya ta ce mutane suna alaqanta su da irin rawar da suke takawa a cikin fina-finai ko wasan kwaikwayo wadda kuma hakan baya nuna cewa halinsu na ainihi kenan.

Ta kara da cewa irin wannan kalon da ake yiwa jaruman fina-finai yasa mazaje ke fargabar zuwa neman aurensu wadda hakan yasa 'yan mata marasa aure ka kara yawa a masana'atar fina-finan.
Har ila yau, jarumar ta ce maza na yiwa matan da suka waye kallon marasa tarbiya.
A cewarta, tun kafin da shiga masana'antar fim akwai mazaje da yawa da suka fada mata cewar suna son ta da aure amma wayewarta ne basu tsoro.

"Ta yaya kawai mutum zai yanke hukuncin cewar ni ba ajinsa bane ba tare da ya min magaba ba, a kasar Hausa ne kawai ake yiwa macen da ta waye kallon mara tarbiya," inji Nayo.

Nayo ta bayyana cewar akwai lokacin da ta yi niyyar aure kuma wato gwagwon ta yi mata tambaya cewar har ta gama girman kan ta ne za tayi aure.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: