Sau ukku yana barazanar zai sake ni, ina rokon kotu ta raba aurenmu - Hauwa Musa
Wata mata mai suna Hauwa Musa, ta bukaci wata kotun shari'a da ke Kaduna, da ta warware auren da ke tsakaninta da mijinta saboda ya yi mata barazanar sakinta har sau ukku
- Ta roki kotun, da ta tabbatar da wannan saki, ta hanyar rubutawa a rubuce, tare da bani ikon rikon yaran da muka haifa guda biyar
- Mai shari'ar, Musa Saad, ya dage sauraron karar har sai 5 ga watan Nuwamba, don baiwa miji da matar damar gabatar da wakilai ko shaidunsu
Wata mata mai suna Hauwa Musa, ta bukaci wata kotun shari'a da ke Magajin Gari, Kaduna, jihar Kaduna, da ta warware auren da ke tsakaninta da mijinta Hamza Abdullahi. A cewar Hauwa, ta gabatar da wannan bukatar ne saboda mijin nata ya yi mata barazanar sakinta har sau ukku.
Bisa rahoton da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya fitar, Hausa ta shaidawa kotun cewa, tun a baya mijin ya dara furta cewa zai saketa har sau biyu, kafin a watan Satumba ya cike kalmar cewa zai saketan a karo na ukku.
Ta shaidawa kotun cewa tun da dai har mijin nata ya yi ikirarin sakin nata har sau ukku, tana dorawa da doka da koyarwar Musulunci, na cewar aurensu na da tangarda, don haka ta ke rokon kotun ta tursasa mijin nata sauwake mata, kuma a rubuta a rubuce.
Hauwa ta ce, "ina rokon wannan kotu, da ta tabbatar da wannan saki, ta hanyar rubutawa a rubuce, tare da bani ikon rikon yaran da muka haifa guda biyar."
A kokarin kare kansa, mijin nata Hamza Abdullahim ya yi ikirarin cewa, ya yi barazanar sakinta ne kawai idan har bata dawo da wuri daga makaranta ba. Ya ce, ya yi wannan barazanar sakin ne kawai saboda akwai wani lamarin gaggawa da ya taso a gidan da ke bukatar matar ta zo da gaggawa.
"Na yi mata barazanar cewa ta dawo kafin mintuna 30 ko na sake ta, kuma ta dawo cikin mintuna 21," a cewar sa.
Mai shari'ar, Musa Saad, ya dage sauraron karar har sai 5 ga watan Nuwamba, don baiwa miji da matar damar gabatar da wakilai ko shaidunsu.
0 comments: