Monday, 12 November 2018

Dattijo mai shekaru 65 ya gamu da ajalin sa a dakin wata Budurwa. - a garin Anambara




Mun samu wani labari mai ban mamaki daga Jaridar Vanguard cewa wani mutumi mai shekaru 65 a Duniya ya mutu wajen kwanciya da wata Budurwa a wani otel a Ranar Asabar dinnan da ta wuce.

Wannan mutumi mai suna Obi Nwoda ya shiga daki ne da wata Budurwa mai shekara 34 a wani katafaren otel a cikin Garin Awka da ke Jihar Anambra. Yanzu dai an sanar da Jami’an tsaron da ke Yankin wannan magana.

Tuni aka sheka da gawar wannan Mutumi zuwa wani babban asibiti da ke wajen Garin na Awka inda aka iske ya cika. Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda na Jihar Anambra Mohammed Haruna ya tabbatar da faruwar wannan abin al’ajabi.

Kamar yadda mu ka samu labari, bayan an ga wannan Bawan Allah ya shiga gargara a dakin wannan Mata ne aka tafi da shi asibiti. Odion Ekeinde ne yayi kokarin kai wannan Dattijo asibiti a sa’ilin da ya shiga wannan mawuyacin hali.

Babban Jami’in ‘Yan Sandan, DPO Haruna ya bayyana cewa akwai alamar tambaya game da mutuwar wannan tsoho wanda hakan ya sa ‘Yan Sandan su ka damke Budurwar da ke tare da wannan Dattijo a lokacin da abin ya auku.

Budurwar tace Dattijon yana tare da ita ne a lokacin da ya kife. Yanzu haka dai Jami’an tsaro su na rike da wannan mata inda ake gudanar da bincike a asibiti game da yadda ajali ya auko ma Dattijon kwatsam.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: