Tuesday, 13 November 2018

Sunayen jaruman fina-finan Hausa 15 da ke yiwa shugaba Buhari kamfen a kakar zaben shekara 2019

Sunayen jaruman fina-finan Hausa 15 da ke yiwa shugaba Buhari kamfen a kakar zaben shekara 2019


A yayin da siyasa ke cigaba da mamaya da ratsa jiki da harkokin jama'a, an yi sharhi a kan yadda goyon bayan Atiku da Buhari ya raba kan jaruman Kannywood

- Yin sharhin ya biyo bayan ganin yadda jaruman ke fitowa fili domin nuna goyon bayansu ga dan takarar da su ke ra'ayi
- Sai dai har yanzu ba a san ina wasu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Rahama Sadu, Hadiza Gabon da Nafisa Abdullahi su ka saka gaba ba
Masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ta bawa shugaba Buhari muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasara a zaben shekarar 2015.

Jaruman fina-finan Hausa da mawaka sun sha halartar taron jam'iyyar APC da yakin zaben Buhari domin nuna goyon bayansu. Kazalika mawaka sun rera ma sa wakoki.
Sunayen jaruman fim din Hausa 15 da ke yiwa Buhari kamfen

Sai dai yanzu fitowar Atiku a PDP ta janye wasu jaruman fina-finan.
Daga cikin jaruman Kannywood da har yanzu ke tare da Buhari akwai;

1. Adam A. Zango
2. Nura Hussain
3. Yusuf Haruna (Baban Chinedu)
4. Jamila Nagudu
5. Halima Atete
6. Rukayya Dawayya
7. Bello Muhammad Bello (BMB)
8. Dauda Kahutu Rarara (Mawaki)
9. Nazifi Asnanic (Mawaki)
10. El-Mu'az Birniwa (Mawaki)
11. Fati Nijar (Mawakiya)
12. Mawaki Aminu Ladan (ALA)
13. Hussaini Danko (Mawaki)
14. Fati Shu'uma
15. Rabi'u Rikadawa

Ragowar jarumar fim din Hausa irinsu Ali Nuhu, Rahama Sadau, Hadiza, Sadiq Sani Sadiq, Nafisa Abdullahi, da sauransu ba su bayyana dan takarar da su ke goyon baya ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: