EFCC ta cafke zinare na N211m a Lagos
Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annato ta yi ikirarin cewa jami'anta sun kama gwala-gwalai da farashinsu ya kai N211m a filin jirgin saman Lagos.
Wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Mr Tony Orilade, ya aike wa manema labarai ta ce an yi niyyar kai gwala-gwalan ne birnin Dubai.
A cewar Mr Orilade, an kama mutumin da ke dauke da zinaren kuma tuni jami'an hukumar suka tsare shi.
"Sakamakon bayanan sirrin da muka samu, ranar tara ga watan Nuwamba, 2018 jami'anmu sun gano gwala-gwalai mau nauyin kilogiram 35 a hanyar shiga jirgi ta filin jirgin saman Lagos kuma yanzu EFCC na tsare da mutumin da ke dauke da gwala-gwalan."
Yanzu haka ana gudanar da binci domn gano wadanda ke da hannu wajen yunkurin fitar da wadannan gwala-gwalai ba bisa ka'ida ba ko da yake mutumin da aka kama yana bai wa jami'anmu hadin kai wurin bincike, in ji EFCC.
A watan Maris na 2017 ma EFCC ta kama wadansu jakuna dauke da zinaren da ya kai N49n a filin jirgin saman Kaduna inda ake shirin fitar da shi daga kasar.
Wednesday, 14 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: