Subahannalah:- Iftila'i ya fada jahar Kano: Gobara ta lamushe wani gini da shago Rijiyar Zaki
- Hukumar 'yan kwana kwana ta ce wata gobarar da ta tashi a Larabar nan, ta lakume wani gini da shago a rukunin gidaje na Rijiyar Zaki da ke cikin kwaryar Kano
- Mai magana da yawun hukumar 'yan kwana kwana ta jihar, Alhaji Saidu Mohammed, ya ce gobarar ta tashi ne daga misalin karfe 10:36 na safiyar 14 ga watan Nuwamba
- Sai dai, ya shawarci jama'a, da su yi taka tsantsan musamman a lokutan bazara da kuma kauracewa amfani da kayayyakin da ka iya haddasa gobara a cikin al'umma
Hukumar kai daukin gaggawa a wuraren da gobata ta afku, ('yan kwana kwana) ta jihar Kano, ta ce wata gobarar da ta tashi a safiyar ranar Larabar nan, ta lakume wani gini da shago a rukunin gidaje na Rijiyar Zaki da ke cikin kwaryar Kano.
Mai magana da yawun hukumar 'yan kwana kwana ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kano, ya ce gobarar ta tashi ne daga misalin karfe 10:36 na safiyar Laraba, 14 ga watan Nuwamba.
Ya ce gobarar ta shafi dakuna 6 a cikin gidan yayin da ake ci gaba da bincike kan dalilin tashin gobarar.
Iftila'i ya fada jahar Kano: Gobara ta lamushe wani gini da shago Rijiyar Zaki
"Mun samu kuran gaggawa a safiyar yau (Laraba) daga Mallam Gambo Usman, da misalin karfe 10:36 na safe, cewar gobara ta tashi a wannan gida. Da jin wannan rahoto, muka gaggauta tura motocin kashe gobara tare da jami'anmu wurin da lamarin ya afku da misalin karfe 10:42 don kashe wutar," a cewar sa.
Sai dai, ya shawarci mazauna gidaje a jihar Kano dama kasar baki daya, da su yi taka tsantsan musamman a lokutan bazara da kuma kauracewa amfani da kayayyakin da ka iya haddasa gobara a cikin al'umma.
Ya ce ya zama wajibi ya bayar da wannan shawarar duba da cewa lokutan sanyi na ci gaba da gabaotwa, don haka ya kamata mutane su yi taka tsan-tsan da kayayyakin da ka iya hadda tashin gobara musamman ma kauracewa barin kayan wutar lantarki a kunne idan ba za ayi amfani da su ba.
0 comments: