Wednesday, 21 November 2018

Hukumar 'yan sanda ta bayyana abinda ya haddasa rikicin Bauchi





Hukumar 'yan sanda a jihar Bauchi ta bayyana cewar rikicin da ya barke ranar Lahadi a unguwar Yelwa da ke garin Bauchi, ba shi da alaka da addini ko kabilanci.

Hukumar ta ce sabani ne tsakanin wasu kungiyoyin matasa biyu da ta rikide zuwa rikici.

Wannan bayanai na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun DSP Kamal Datti Abubakar, kakakin rundunar, da hukumar ta fitar a yau, Laraba.

Sanarwar ta kara da cewar, hukumar 'yan sanda na wannan bayanai ne a matsayin raddi ga labaran da ke yawo a kafar sada zumunta da ke nuna cewar rikicin na da alaka da addini ko kabilanci.

"Muna son sanar da jama'a cewar duk wani rahoto da ke nuna cewar an samu rikicin addini ko na kabilanci a jihar Bauchi ba gaskiya ba ne. Irin wadannan rahotanni sun samo asali ne daga jama'ar da basa son zaman lafiyar jama'a.

"Binciken hukumar 'yan sanda ya tabbatar da cewar rikicin ya faru ne tsakanin wasu kungiyoyin matasa ta unguwar Yelwa da ke cikin garin Bauchi.

"Rigima ce tsakanin samari a kan budurwa a wurin wani biki, shine rikicin da ya shafi wasu ma su wucewa ta hanyar. Lamarin ya faru ne da misalin 10:00 na daren ranar Lahadi.

"Hukumar 'yan sanda ta samu rahoto a kan lokaci kuma nan da nan ta kwantar da rikicin," a cewar jawabin.


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: