Wednesday, 21 November 2018

Rikici ya Barke a Bauchi , Bisa Gwamnati tasanya dokar hana zirga-zirga




Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta sanya dokar hana fita da daddare sakamakon rikicin da ya barke a birnin Bauchi.

Mai magana yawun gwamna Abubakar Mohammed, Malam Ali M. Ali, ya shaida wa BBC cewa "an hana fita tsakanin karfe bakwai na dare zuwa shida na safiya" sanadiyar fadan da ya kai ga mutuwar mutum uku.

Lamarin ya faru ne lokacin da aka samu rashin jituwa tsakanin matasan da suke bikin tunawa da ranar haihuwa kan wata budurwa, amma fadan ya rikide zuwa na kabilanci da siyasa.

Dokar hana fitar ta shafi unguwannin Kagadama da Lushi da Tsakani da Kusu da kuma Anguwan Ngas da ke yankin Yalwa a cikin birnin na Bauchi.

Wanne ne karon farko da aka samu irin wannan yamutsi da ya yi dalilin mutuwar mutane tun da gwamnan jihar ya hau kan mulki shekara uku da rabi da suka wuce, in ji mai magana da yawunsa.
Ya yi kira da mazauna jihar su ci gaba da zama lafiya da juna.

Tuni dai gwaman jihar ya kai ziyara yankunan da lamarin ya shafa.
Gwamna M A ya kuma ce gwamnati za ta yi iyakar kokarinta don ganin rikicin bai yadu a wasu wuraren ba.

Jihar Bauchi dai na daga cikin jihohin da ba a faye samun tashe-tahsen hankula kowane iri ba a Najeriya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: