TAMBAYA
malam idan mutun andaura mashi aure ranar dayashiga dakin matar shi maiye nafarko dazaiyi?
AMSA
Idan aka kaiwa mutum Amarya, Budurwa ce ko Bazawara, to tin daga wannan Ranar wannan mutumin ya zama ANGO kenan, wannan shine sabon sunan da Al'ada ta kirashi dashi, har zuwa lokacin da wannan Amaryar Zata Haihu, anan ne zakaji ance Amarya ta haihu.
A daidai lokacin da Ango ya shiga dakin Amaryarsa, duk da cewar shi Angon da ita amaryar suna cikin Shaukin juna kafin shaidan ya fara yin tasiri Akansu. To Abinda zai fara yi idan ya shiga dakin Amaryarsa wadda Allah madaukakin sarki ya Halatta masa ita, Sai ya bude labulen dakin Amaryarsa, idan mai kunya ce zai sameta cikin lullubi ta Buya masa ta hanyar rufe ido da duk wani abu da ya nuna cewar tana jin kunyar mijinta.
Idan Ango ya bude labulen kofar dakin Amaryarsa sai ya shiga da kafar dama, sannan yace
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKATUH, YA AHLU BAITIY.
Haka hadisi ingantacce ya nuna ruwayar Muslim, idan manzon Allah saw zai shiga dakin kowacce daya daga cikin matansa sai yayi Mata irin wannan sallamar.
Wato AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GAREKI IYALIN GIDAN MANZON ALLAH SAW.
Bayan sallama sai Ango ya bude mayafin da Amaryarsa ta lullube fuskarta dashi. Sannan yayi Mata Umarnin da tayi Alwala, sai suyi sallah Raka'a biyu, ya shiga gaba tana binsa a baya. Idan sun Gama sallar sai ya umarceta da ta zauna a gabansa, idan ta zauna sai ya dora tafin hannunsa Akanta, sai yayi Addu'ah kamar haka
ALLAHUMMA INNIY AS'ALUKA KAIRIHA WA KAIRI MA FIYHA, WA KHAIRI MA JABALTA BIHA, WA'A'UZU BIKA MIN SHARRIHA WA SHARRI MA FIYHA WA SHARRI MA JABALTA BIHA.
Wato ya Allah ina Rokonka Alkairin wannan baiwar Allah da Alkairin da ka jarrabeta dashi, ina Rokonka ka tsareni da sharrin wannan baiwar Allah da sharrin da ka jarrabeta dashi.
Sannan kuma sai Ango ya yiwa Amarya Nasiha da Alkawarin zai zauna da ita bisa Amana, itama tayi masa Alkawarin Zata zauna dashi a bisa Amana, babu munafurcin juna, babu cin Amanar juna, Babu wulakanta juna. Da yiwa junansu Addu'ar Allah ya kawo musu zaman lafiya ya tsaresu daga sharrin Shaidan. Da dai Sauransu.
Bayan gabatar da wadannan abubuwan Shikenan, Abinda zaizo nan gaba kuma sai Abinda Suka gadama zasu Aiwatar. Komi suka Aikata halak ne, Asalima Lada zasu samu.
Allah shine masani.
Tuesday, 20 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: