Monday, 19 November 2018

Babbar magana: Rundunar soji ta gano sabuwar kungiyar ta'addanci a arewa, hotuna





Hukumar soji ta bayyana cewar ta yi nasarar gano sabuwar kungiyar ta'addanci mai kama da Boko Haram, tare da sanar da gano waye shugaban sabuwar kungiyar JAMA'ATUL NUSRATUL-ISLAMI WAL-MUSLIMINA.

Abul-Fadl Iyad Gali ne mutumin da hukumar soji ta ce ke jagorantar sabuwar kungiyar.

Hukumar soji ta ce zata yi amfani da kayan aikinta na kimiyya domin gano duk inda shugaban kungiyar ya ke tare da dakile aiyukan ta'addanci da su ke ikirarin fara aikatawa a Najeriya.

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewar ta yi nasarar kashe Sale Ahmad Sale, babban jami'in watsa labarai na kungiyar Boko Haram tsagin Albarnawi.

Tsagin kungiyar Boko Haram da ke karkashin jagorancin Albarnawi na da alaka da kungiyar ta'addanci ta IS. Tuni tsagin ya canja suna daga Boko Haram zuwa ISWAP (kungiyar IS reshen nahiyar Afrika ta yamma).

Kisan jami'in yada labaran na daga cikin aiyukan dakarun sojin Najeriya da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno na kakkabe dukkan manyan jami'an kungiyar Boko Haram.


A sanarwar da hukumar soji ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce tana matukar alfahari da kisan Sale bisa la'akari da irin matsauinsa a tsarin shugabanci na kungiyar Boko Haram, tare da bayyana cewar hakan na nuni da cewar nan ba da dadewa ba zasu kai ga cimma ragowar shugabannin kungiyar.

Sanarwar ta kara da cewa, kafin a kashe shi, Sale ya jagoranci kai wasu hare-hare da su ka kai ga asarar rayuka a baya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: