Zargin damfara: EFCC ta gurfanar da dan takarar gwamna a Kano
Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da Abdulsalam Abdulkareem, dan takarar gwamna a Kano a karkashin tutar jam'iyyar GPN, bisa zarginsa da yin zambar kudi dalar Amurka miliyan $1,320,000.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da Abdulkareem bisa tuhumar sa da aikata laifuka 9 ma su nasaba da damfara, zamba, cin amana da sauransu.
Wani mutum ne ya shigar da korafin dan takarar bisa kan cewar ya zambace shi adadin kudin da sunan za su yi wani kasuwanci a shekarar 2014.
Mai korafin ya kara da cewar Abdulsalam ya hadu da hadiminsa a kasar Kuwait domin tattauna harkar kasuwanci da ya zo da ita.
Bayan kammala tattaunawa a kasar Kuwait ne sai wani kamfani mallakar mutumin da ya shigar da korafin ya kira Abdulsalam Najeriya tare da bashi adadin kudin da ya ambata domin shiga kasuwancin hadin gwuiwa.
Sai dai bayan gurfanar sa gaban kotu a yau, Litinin, Abdulsalam ya musanta dukkan zargin da ake yi ma sa.
Bayan kotu ta amince da bayar da belin Abdulsalam a kan miliyan N100m da kuma gabatar da wadanda za su tsaya ma sa, kotun ta daga sauraron karar zuwa ranakun 29 da 30 na watan Janairun shekarar 2019.
Monday, 19 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: