Makarantar da aka kulle saboda dalibai sun saka hijabi
Kamar yadda shugaban makarantar, Phebean Olowe, ya bayyana, an rufe makarantar ne saboda rashin amincewa dalibai mata musulmi su saka hijabi zuwa makaranta.
Makarantar sekandare ta University of Ibadan International School dake garin Ibadan nan jihar Oyo ta rufe makaranta saboda wasu dalibai sun saka Hijabi.
Kamar yadda shugaban makarantar, Phebean Olowe, ya bayyana, an rufe makarantar ne saboda rashin amincewa dalibai mata musulmai na su saka hijabi zuwa makaranta.
A cikin wata wasika da suka tura ma mahukuntan makarantar a ranar 9 ga watan Nuwamba, iyayen yara karkashin kungiyar iyayen dalibai na makarantar (PTA) sun sanar cewa yaran su zasu fara saka hijabi zuwa makarantar.
Kungiyar tayi ikirari cewa bayan ga ibada yara mata na da damar saka hijabi bisa ga yadda dokar kasa ta tanadar.
Sai shugaban majalisar koli na makaranatar
Farfesa Abideen Aderinto ya soki matakin da kungiyar ta dauka.
Yace makarantar ba ta gwamnati bace don haka suna da damar kafa dokoki matukar iyayen makaranta sun amince da shi.
"Duk wanda ke son canja wata doka a makarantar sai ya bi ta hanyoyin da suka dace," inji Aderinto.
Sunday, 18 November 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: