Sai Buhari ya sauka daga mulki zai iya gane munafukan sa - Sanata Shehu Sani
Dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ba yadda za'ayi shugaba Buhai ya gane hakikanin masu kaunar sa tsakanin da Allah sai ya sauka daga kan mukaman sa wata rana a nan gaba.
Sanata Sani dai yayi wannan hasashe ne a shafin sa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya bayyana cewa dayawa daga cikin masu yi masa dadin baki a yanzu munafunci ne kawai amma abun da ke zuciyar su ya sha banban da na bakin su.
ko da yake Sanatan Sani bai fito fili ya bayyana da su yake ba, ana kyautata zaton da wasu yake makusantan sa a fadar mulkin da kuma wasu kusoshi a jam'iyyar dake jagoranta ta APC.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai Sanatan ya yi kaca-kaca da masu kiran kan su 'yan amutun shugaban inda yake cewa da yawan su suna fadar haka ne kawai don cimma wata manufa tasu ta siyasa
0 comments: